Mutane ke janyo kashi 95 na sauyin yanayi

Masana'antu ke fitar da gurbatacciyar iska
Image caption Gurbatacciyar iskar da masana'antu ke fitarwa na haddasa dumamar yanayi

Masana kimiyya na Majalisar Dinkin Duniya, sun ce sun gamsu da cewa, bil'adama ne ke haddasa dumamar yanayi.

Wani sabon rahoton kwamitin hadin gwiwa na kasa-da-kasa a kan dumamar yanayi, ya nuna yadda duniya ta kara dumama tun daga shekarar 1950.

Rahoton yace, ya tabbatar bil'adama ne ke haddasa kashi 95 cikin dari na matsalar.

Masanan kuma sun yi gargadin cewa yawan ruwan teku zai tumbatsa da sentimita 82 nan da karshen wannan karnin.

Sun kuma kara da cewa dakatar da fitar da gurbatacciyar iska a shekaru 15 da suka wuce, ba zai iya nuna tasiri lamarin na lokaci mai tsawo mai zuwa ba.