An sanar da tallafin £9.5m ga kasashe biyar

Ambaliyar ruwa a Pakistan
Image caption Ambaliyar ruwa a Pakistan

Wani hadin gwiwa tsakanin asusun tallafi na Musulunci a London da hukumar raya kasashe ta Birtaniya zai samar da fam miliyan 9 da rabi, domin aiwatar da wani shirin tallafi.

Shirin zai taimaka wa mutane kusan rabin miliyan da ke fuskantar hadarin fari ko ambaliyar ruwa a wasu sassan duniya.

Sanarwar ta ranar Juma'a ta ce taimakon zai shafi mutanen dake kasashe biyar wato Nijar da Kenya da Pakistan da Yemen da kuma Bangladesh.

Tuni matsalolin fari da ambaliyar ruwa su ka fara shafar dubban mutane a wasu daga cikin kasashen.