Kenya: Mayaka sun kama shago a Westgate

Image caption Mutane da dama sun rasa 'yan uwansu

Mayakan da suka kaddamar da hari a cibiyar kasuwanci ta Kenya sun dauki hayar shago a cibiyar makwanni kafin su diranma wajen, kamar yadda majiyoyin tsaro suka shaidawa BBC.

Hakan ne ya basu damar amfani da cibiyar Westgate har suka tattara makamai da alburusai a ciki.

Mutane 67 ne suka mutu a kwanaki hudu da aka shafe ana artabu, a yayinda kungiyar agaji ta Red Cross ta ce akwai karin mutane 61 da suka bace.

Binciken da BBC ta gudanar ya nuna yadda 'yan bindigan suka kaddamar da harin a Westgate, akwai sakaci sannan dakuma cin hanci da rashawa tsakanin jami'an tsaro ne ya basu damar cin karensu babu babbaka.

'Sakacin jami'an tsaro'

Domin karbar hayan shago, mayakan na bukatar katin shaida na bogi wanda jami'an gwamnati marasa gaskiya suka basu.

Majiyoyin tsaro sun bayyanawa BBC cewar a ranar da aka kaddamar da harin, an sauke masu tsananin kishin Islama a cikin motoci biyu a wajen cibiyar Westgate kafin su kutsa cikin rukunin shagunan.

Ana zargin sun kafa sansani ne a hawa na farko a Westgate sannan a daren ranar Asabar sun sauya inda suka boye.

Sun yi amfani da manyan bindigogi wajen harin.

Kungiyar Alshabab ta ce itace ta kai harin saboda dakarun Kenya da suka je Somalia don fafatawa dasu.

Akwai dakarun Kenya 4,000 a Somalia wadanda ke taimakawa gwamnati a Moghadishu don murkushe ayyukan 'yan Alshabab.

Kungiyar wacce aka haramta a Amurka da Birtaniya ana tunanin tana da mayaka tsakanin 7,000 zuwa 9,000.

Karin bayani