Mali: Azbinawa sun yi barazana kan sulhu

Image caption Shigar sojan Faransa ne ta bai wa sojojin gwamnati damar komawa garin Azbinawa na Kidal

Azbinawa 'yan aware a arewacin Mali sun ce za su jingine shiga wata tattaunawar kawo zaman lafiya, suna zargin gwamnati da rashin mutunta yarjejeniyar da aka cimmawa a wata Yuni.

Wasu kungiyoyin Azbinawan guda uku da ke wata ganawa a Burkina-Faso sun yi kiran da a yi wani taron gaggawa na dukkan bangarorin da ke cikin yarjejeniyar.

Wannan matakin dai wani ci-baya ne ga sabon zababben shugaban kasar Mali Ibrahim Boubakar Kaita, wanda ke kokarin sake hada kan kasar bayan wani juyin mulki da kuma tawaye a shekarar bara.

An cimma yarjejeniyar zaman lafiyar ne bayan shigar da sojan Faransa suka yi wajen yaki da 'yan tawaye masu kishin addinin musulunci a arewacin Mali.

Karin bayani