Takaddama kan albashin 'yan majalisar Najeriya

Image caption A baya dai wasu sun yi kiran da rushe Majalisar Dattawan kasar a bar ta wakillai kawai domin rage kudaden da ake kashewa kan majalisun.

Wasu kungiyoyin matasan a Najeriya na fafutukar ganin 'yan majalisun dokokin kasar da sun fito su bayyana yawan kudaden da ake biyan 'yan Majalisun don tafiyar da ayyukansu wadanda matasan ke jin sun zarce kima.

Wasu kungiyoyin sun gudanar da zanga-zangar lumana a harabar Majalisar dokokin kasar a Abuja ranar Alhamis inda suka ce tilas 'yan Majalisar su fito su shaidawa 'yan kasar yadda suke gudanar da wasu ayyukansu.

Da ma dai ana jin cewar 'yan Majalisun dokokin Najeriyar na lakume makudan kudade a matsayin albashi fiye da wasu takwarorinsu na kasashen duniya.

Sai dai daya daga cikin 'yan Majalisar Wakilan kasar, Mr. Jagaba Adams Jagaba, ya ce kudaden da ake biyan 'yan Majalisar ba su zarce kowace irin ka'ida ba.

'' Wato da sun san abin da ke tafiya kasar nan da ba su tashi suna wannan zanga-zanga ba; ai kudaden majalisa an ware su ne domin a yi yaki don talaka'' inji Mr. Jagaba wanda ke shugabantar kwamitin kula da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa na Majalisar wakilan kasar

Karin bayani