Za a yi babbar zanga-zanga a Sudan

Masu zanga zanga a Sudan
Image caption Kudin shigar Sudan ya ragu, tun bayan samun 'yancin kan Sudan ta Kudu shekaru kusan biyu da suka wuce

Masu fafutuka a Sudan, sun yi kira da a fito babbar zanga-zanga a ranar Juma'a, domin bijire wa gwamnati a kan karin farashin man fetur.

An tura sojoji su ba da kariya ga gidajen mai da gine-ginen gwamnati a Khartoum babban birnin kasar da sauran wasu birane.

Hukumomin na Sudan sun ce mutane 29 suka mutu a zanga-zangar, amma kungiyoyin kare hakkin dan adam dake cikin kasar sun ce kimanin mutane dari ne aka kashe, akasarin su kuma jami'an tsaro ne suka harbe.

Wasu masu zanga-zangar na kira da a hambarar da Shugaba Omar El-Bashir.

Karin bayani