Tafida ya yi tsokaci game da rikicin PDP

Jakadan Najeriya a Birtaniya, Dalhatu Sarki Tafida
Image caption Jakada Tafida ne ya jagoranci yakin neman zaben shugaba Jonathan a shekarar 2011

Jakadan Najeriya a Birtaniya, Dalhatu Sarki Tafida ya ce kamata ya yi a duba korafe-korafen 'ya'yan jam'iyyar PDP mai mulkin Najeriyar da suka balle.

A hirarsa da BBC Hausa, Alhaji Tafida ya kuma ce Shugaba Goodluck Jonathan na da 'yancin tsayawa takara a shekarar 2015.

Sannan ya bayyana damuwa game da rikicin da jam'iyyar ke fuskanta, ko da yake ya nuna cewa abu ne mai wucewa, idan an so hakan.

Jakadan ya bayyana cewa ya ji batun yarjejeniyar da aka ce shugaba Jonathan ba zai tsaya takara a zabe mai zuwa ba, sai dai ba da shi aka yi ba, kuma a shirye yake ya goyi bayan duk wanda jam'iyyarsa ta tsayar.