Gwamnatin Italiya ta shiga tsaka mai wuya

A kasar Italiya, Ministoci daga jam'iyyar Silvio Berlusconi ta masu matsakaicin ra'ayin rikau, PDL sun bada sanarwar ficewa daga gwamnatin hadin gwiwa.

Jam'iyyar ta ce sun yi hakan ne a matsayin martani ga barazanar da Praminista Enrico Letta yayi na yin murabus, idan ya gaza samun cikakken goyon baya a kuri'ar nuna goyon bayan da za a kada masa.

Guliemo Epifani, shi ne jagoran jam'iyyar Mr Letta Democratic.

Wakilin BBC a Roma ya ce bisa dukkan alamu hakan na nuna alamun karshen gwamnatin a yadda take a yanzu, da kuma yuwuwar shirya sabon zabe.