Fulani sun ce an yi watsi da ilimin 'ya'yansu

Fulani Makiyaya a Nijeriya
Image caption Kungiyar Miyatti Allah ta Nijeriya ta koka da cewa an yi watsi da ilimin 'yayan makiyayan

A Najeriya Kungiyar Fulani Makiyaya ta kasa Miyatti Allah ta koka da abinda ta kira watsi da aka yi da ilimin 'ya'yan makiyaya wanda a da ke karkashin kulawar hukuma ta musamman ta Nomadic Education.

Kungiyar ta Miyatti Allah tace, siyasa ce ta sanya aka mayar da alhakin kula da ilimin Fulanin makiyayan karkashin kulawar gwamnatin Tarayya - wadda ita kuma ta mayar da shi karkashin kulawar kananan hukumomi da hukumar kula da ilimin firamare ta jihohi.

A hirar su da BBC Alhaji Hussain Yusuf Bosso, Shugaban kungiyar ta Miyatti Allah shiyyar Arewa ta tsakiya ya bayyana cewar tunda sun san muhimmancin da suke da shi ga kasar, za su yi yaki domin ganin an mayar wa hukumar kula da ilimin makiyayan martabar ta.