An samo gawarwaki 16 a hadarin kogin kwara

Kwale kwale
Image caption Kwale kwale

A Nijeriya, wani jirgin ruwa dauke da mutane akalla dari da hamsin ya rabe gida biyu, ya kuma nutse a kan kogin Kwara.

Ma'aikatan ceto sun shaida mana cewa kawo yanzu sun samu fito da kimanin gawarwakin mutane goma sha shida yayin da ake ci gaba da laluban sauran mutanan.

Hadarin jirgin dai ya faru ne a garin Malale akan hanyarsa ta zuwa jahar Kebbi.

Wadanda suka ganewa idanunsu abinda ya faru sun ce kimanin mutane talatin ne aka samu ceto su da rai.

A 'yan watannin baya bayannan dai anyi ta samun hadarin jiragen ruwa a arewacin Najeriyar, inda ake cewa daukar yawan mutanan da suka fi karfin jirginne a yawancin lokuta ke haddasa hadarin.

Ko a kwanakin baya ma wani jirgin daukar amarya ya yi hadari a jahar Kano inda aka samu asarar rayuka da dama.