Zanga zanga a Sudan ta yi kamari

An harba hayaki mai sa hawaye a kan wasu masu zanga zanga dake halartar jana'izar wasu da aka kashe a lokacin wata tarzoma a Khartoum, babban birnin Kasar Sudan.

Daruruwan mutane sun rika rera wakokin la'antar shugaban kasar ta Sudan, Umar al Bashir, a jerin irin zanga zangar da aka fara cikin makon jiya, bayan da gwamnati ta janye tallafi kan farshin man petur.

'Yan sanda sun ce mutane hudu sun rasu a zanga zangar da aka yi jiya, Juma'a, suna kuma dora laifin kisan a kan wasu 'yan bindiga da ba shaida ba.

Hukumomi na cewa akalla mutane talatin ne suka mutu tun bayan fara tarzomar, amma likitoci da wasu masu fafutuka na cewa yawan wadanda aka kashen ya zarta hakan nesa ba kusa ba.