An daure 'yan Shia a Bahrain

'yan shia na bahrain
Image caption Wadanda aka daure 'yan kungiya ce da ke zanga zangar kyamar gwamnati.

Wata kotu a Bahrain ta yanke hukuncin da ya kai na daurin shekaru 15 a gidan kaso kan wasu 'yan shia 50.

Bisa zargin kafa wata kungiyar 'yan adawa ta sirri da nufin kifar da gwamnati.

16 daga cikin mutanen an an daure su shekaru 15, wasu mutanen hudu 10, ragowar kuma shekar15.

Talatin daga cikin wadanda ake zargin sun halarci zaman kotun, sun kuma ce za su daukaka kara.

Sauran mutanen, an yanke hukuncin ne a bayan idanunsu, domin ba sa kasar.

Wannan shi ne mataki na baya baya da hukumomin Bahrain suke dauka kan kungiyar sha hudu ga watan Fabrairu.