An kai wa Kurdawa hari a Iraqi

harin bam din mota a Iraqi
Image caption Wadannan hare hare na daga cikin na farko cikin shekaru shida a yakin na Kurdawa

An kai hare haren bam na mota a wasu yankuna na Irbil, hedkwatar yankin Kurdawa mai cin gashin kai da ke Iraqi.

Wasu rahotanni na cewa mutane akalla shida suka mutu a hare haren.

wadanda aka hari hedkwatar ayyukan tsaron yankin na Kurdawa da kuma ma'aikatar cikin gidansu.

Rahotanni daga yankin na cewa wasu daga cikin maharan sun yi shiga irin ta ma'aikatan asibiti.

Sun kuma yi amfani da motar daukar marassa lafiya wajen dasa daya daga cikin bama baman.