Gwamnatin Italiya ta rushe

Image caption Al'ummar italy sun wayi gari suna neman sanin abin da ya kai ga rushewar gwamnatin kasar su a cikin dare.

Gwamnatin hadin-gwiwa ta kasar Italy ta rushe bayan Ministoci na jam'iyyar masu ra'ayin rikau ta tsohon Faraminista Silvio Berlusconi sun yi murabus.

Ministocin 6 sun yi murabus ne ranar Assabar domin nuna rashin amincewa da barazanar da Faraminista Enrico Letta na jam'iyyar masu ra'ayin sauyi yayi ta yin murabus idan suka ki bashi goyon bayan a kuri'ar nuna goyon baya da ke tafe.

Ana sa ran Shugaban Italiya Giorgio Napolitan ya gana da Faraminista Enrico Letta yau lahadi domin tattauna rushewar gwamnatin hadakar. A zaman shugaban kasar, dole ne Mr. Napolitano yayi nazarin ko ya ba da umarnin kafa sabon gamin-gambiza ko kuma ya kira da a yi sabbin zabuka.

A halin yanzu dai shugaban kasar maras-ikon-zartarwa, Giorgio Napolitani ya zamo mutum mai muhimanci ainun. Shi ne ke da wuka-da-nama yanzu wajen yanke shawarar a rusa majalisar dokokin kasar ko a'a.

Karin bayani