Zaben 'yan majalisa da kansiloli a Kamaru

Taswirar Kamaru
Image caption Taswirar Kamaru

A Kamaru an rufe rumfunan zabe bayan da jama'a suka fito kada kuri'a a zaben 'yan majalisar dokoki da kuma kansiloli.

Rahotanni na cewa, duk da ruwan saman da yi a wasu sassan kasar, jama'a da dama sun fito domin kasa kuri'arsu.

'Yan majalisar dokoki dari da tamanin da kuma kansiloli dubu goma ne ake sa ran zaba.

A zabukan baya dai 'yan adawa sun sha zargin gwamnatin Paul Biya da rashin tsaida takamaiman lokacin zaben 'yan majalisa, don dai jam'iyyar RDPC mai mulki ta sami galaba.

Amma jam'iyyar ta RDPC ta sha musanta wannan zargi.