Ba mu gamsu da dokar ta-baci ba —Geidam

Image caption Gwamnan jihar Yobe, Ibrahim Geidam

Gwamnatin jihar Yobe ta nuna rashin gamsurta game da yadda gwamnatin Tarrayyar kasar ke aiwatar da dokar ta-baci a kokarin tabbatar da tsaro.

Gwamnan jihar, Alhaji Ibrahim Giedam, ya ce ya kamata hukumomin tsaro a kasar su sake duba irin yadda suke gudanar da ayyukansu domin kare lafiyar al'umma.

Gwamnan Geidam ya ce "muna ganin sojoji da motoci masu sulke suna kai da kawowa, to amma har yanzu ba mu ga wani abu takamaimai ba a kasa".

Ya kara da cewar, "Ina kira ga jami'an tsaro su tashi tsaye domin yin aikin da mutane suke fatan za su yi".

Gab da asubahin ranar Lahadi ne wadanda ake zargin 'yan Boko Haram ne suka kai wa dalibai hari a jihar Yobe inda suka kashe akalla mutane hamsin.

Karin bayani