'Yan ci-rani sun mutu a gabar tekun Italiya

Image caption Dubban 'yan ci rani ne ke mutuwa a duk shekara a kokarin tsallaka teku

Masu gadi a gabar tekun Italiya sun ce, 'yan ci-rani akalla goma sha uku, 'yan Afirka, sun nutse kusa da gabar ruwan Sicily.

Lamarin ya faru ne bayan da wani jirgin ruwan da ke dauke da mutane fiye da dari da hamsin yayi hadari.

Mutanen suna kokari ne su yi iyo zuwa gabar teku, daga jirgin ruwan da ke cike makil da jama'a daga Eritrea.

Masu gadin gabar tekun sun yi amannar cewa, ma'aikatan jirgin sun tilasta wa wasu daga cikin fasinjojin barin jirgin.

A lokacin bazara dubban 'yan ci-rani ne ke isa kudancin Italiya, a cikin kananan jiragen ruwan da ke cike makil.

Sannan ga 'yan gudun hijirar Syria da su ma suke ta zuwa.

Karin bayani