Gwamnatin Italy na neman amincewar 'yan kasa

Silvio Berlusconi
Image caption Prime Ministan Italia Enrico Letta zai nemi kuriar majalisar dokoki bayan ficewar jam'iyyar Silvio Berlusconi daga gwamnatin

Prime Ministan Italia Enrico Letta ya tabbatar da cewa zai nemi a kada kuri'ar amincewa da gwamnatinsa a majalisar dokoki a ranar laraba a wani yunkuri na kauce ma wasu sabbin zabukka - watanni bakwai kacal da zabukkan da aka gudanar.

Sanarwar ta zo ne bayan Mr Letta ya tattauna da Shugaba Giorgio Napolitano jim kadan bayan faduwar gwamnatinsa ta hada-ka. Mr Napolitanon ya bayyana cewa kiran sabbin zabukan zai yiwu ne kawai idan aka gaza samun wani zaab

Karin bayani