Artabu tsakanin Azbinawa da soji Mali

Image caption Mayakan Azbinawa a Mali

Rahotanni daga garin Kidal dake arewacin Mali na cewa an ci gaba da jin amon harbe harbe a ranar Litinin, a yayinda jama'a ke ci gaba da kasancewa gida.

Hakan dai ya biyo bayan musayar wuta ne da aka soma tun ranar Lahadi tsakanin Azbinawa 'yan aware da kuma dakarun gwamnati.

Dukan bangarorin biyu dai na zargin juna da fara bude wuta.

Kwanaki uku da suka wuce ne dai, kungiyar 'yan tawayen Azbinawa ta bada sanarwar kawo karshen tsagaita wuta tsakaninta da sabuwar gwamnatin Malin karkashin jagorancin, Ibrahim Boubakar Keita.

Karin bayani