'Yan kasuwar Nijar sun yi korafi

Image caption 'Yan kasuwar sun bukaci gwamnati ta tsoma baki

A jamhuriyar Nijar, kungiyar 'yan kasuwa a jihar Maradi ta koka cewa wasu 'yan kasuwa daga kasashen yankin Asia da ke shigo da kayan abinci kasar sun mamaye kusan komai ta fuskar kasuwanci.

'Yan kasuwa na yankin Maradin masu sayar da kaya abinci sun kuma yi zargin cewa lamarin ya kawo musu koma baya ta fuskar ciniki.

'Yan kasuwar sun kuma bukaci hukumomi su tsoma baki cikin wannan lamari.

Hukumomi a jihar dai sun ce za suduba korafe-korafen 'yan kasuwar.

Karin bayani