Fargabar rabuwar kawuna a majalisar nijer

Shugaba Muhammane Issofou na Nijer
Image caption Saboda shigar wasu 'yan siyasa gwamnatin hada-ka a nijer, ana fargabar abinda zai faru idan majalisa ta koma zama nan da makonni biyu

A Jamhuriyar Nijar, a daidai lokacin da ake shire-shiren fara zaman majalisar dokokin kasar a mako mai zuwa, wasu kungiyoyin farar hula sun fara nuna fargabarsu dangane da abinda suka kira alamomin rabuwar kawunan 'yan kasar sakamakon barakar da jam'iyyun siyasar da dama ke fuskanta.

A yanzu dai hankula sun karkata ne ga majalisar dokokin domin ganin yadda za ta kaya tsakanin bangaren shugaban kasar mai cikakken rinjaye da bangaren adawa na ARN wanda ake jin zai samu goyon baya daga jam'iyyar Moden Lumana ta shugaban majalisar dokokin kasar Malam Hamma Amadu wadda ta janye daga kawancen dake mulki na MRN.

Karin bayani