Shakku game da zaman lafiya a Syria

Walid al-Moallem, Ministan harkokin wajen Syria
Image caption Walid al-Moallem, Ministan harkokin wajen Syria

Ministan harkokin wajen Syria, Walid al-Moallem, ya nuna shakku a kan yiwuwar samun cigaba a lokacin taron kawo zaman lafiya a Syriar.

A cikin hira da BBC a New York, inda al-Moallem din yayi jawabi ga babban taron majalisar dinkin duniya, ya ce ba za a sami nasara a shawarwarin kawo zaman lafiyar ba, matsawar kasashen Saudiyya, da Qatar da kuma Turkiyya na cigaba da goyon bayan 'yan tawaye masu dauke da makamai.

Ministan harkokin wajen Syriar ya kuma ce, kasarsa za ta bada hadin kai ga sufetocin da ke da alhakin lalata makamanta masu guba.

To amma ya kara da cewa, wurare bakwai daga cikin sha tara inda aka jibge makaman, suna yankunan da ke hannun 'yan tawaye.