Sabani a Majalisar dokokin Amurka

Majalisar Dokokin Amurka
Image caption Majalisar Dokokin Amurka

Majalisar dattawan Amirka ta yi watsi da wata shawara ta majalisar wakilan kasar, inda 'yan Republican ke da rinjaye, wadda ta danganta kasafin kudin gwamnati da dokar shugaba Obama, ta yin gyara ga tsarin lafiya a kasar.

'Yan sa'o'i kawai suka rage komi ya tsaya cik wajen tafiyar da harkokin gwamnati, saboda ja-in-jar tsakanin majalisun dokokin biyu.

Idan har nan da sha biyun dare (agogon Amirkan) ba a cimma maslaha ba, to kuwa ma'aikatun gwamnati dayawa zasu rufe, wanda hakan zai sa dubun dubatar ma'aikatan gwamnatin tarayya su rasa albashinsu, sannan ba za a yi aikace-aikace masu yawa ba.

Ganin cewa ba alamar sasantawa nan kusa, 'yan jam'iyyar demokrat da wasu 'yan Republican 'yan kalilan, na matsa wa majalisar wakilai kaimin ta amince da wani kudurin