Ba za mu rufe makarantu ba —Gwamnatin Yobe

Image caption Babu sojojin dake galibin makarantu a jihar Yobe

Hukumomi a jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya sun ce ba za su rufe makarantu ba duk da harin da aka kai a Kwalejin koyon aikin gona da ke Gujba.

Akalla mutane hamsin aka kashe a harin da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram da kai wa ranar Lahadi.

Mai bai wa gwamna Ibrahim Gaidam shawara a fannin watsa labarai, Abdullahi Bego, ya shaidawa BBC cewa idan aka rufe makarantun, wadanda ya kira 'yan ta'adda za su ji dadi.

Ya kara da cewa da ma abin da suke so kenan shi yasa suka kai harin.

Malam Bego ya ce ba a samar da tsaro ga dalibai a makarantar koyon aikin gona ta jihar Yoben ba.

Wani dalibi da ya sha da kyar ya shaidawa BBC cewa ya haura ta tagar dakin kwanansu ne, ya tsere.

Ya ce ya fada cikin dimuwa lokacin da ya ga gawarwakin abokansa bayan ya dawo makarantar ranar Lahadi da daddare.

Kungiyar Boko Haram dai ta a baya ta kaddamar da hari a kan makarantu da masallatai da coci a sassan arewacin kasar.

Karin bayani