Sojin Congo sun gama da 'yan tawayen M23

Sojojin Congo
Image caption Sojojin Congo suna murnar samun nasara

Sojojin kasar Congo , wadanda dakarun kiyaye zaman lafiya majalisar dinkin duniya ke mara ma baya, sun fatattaki 'yan tawayen kungiyar M23 daga matattararsu dake gabashin jamhuraiyar Dimokradiyar Congo.

Kame garin Bunagana wanda ke kan iyaka da Uganda, ya faru ne bayan da majalisar dinkin duniya ta kara yawan dakarunta a yankin, ta kuma kara masu ikon amfani da karfi.

Kakakin sojan Uganda Laftanar Kanar Paddy Ankunda ya musanta rahotannin cewa jagoran kungiyar ta m23 , Bertrand Bisimwa ya mika kansa. Ya ce, ya je Uganda ne domin bada gudunmawa a tattaunawar da ake yi, rahotannin da aka bayar cewa yayi saranda, ko ya tsere ba gaskiya ba ne.

Yan tawayen wadanda galibinu 'yan kabilar Tutsi ne da suka sauya sheka daga rundunar sojan kasar, sun dauki makamai ne tun cikin watan Aprlun bara suka kuma rika kwace yankuna cikin sauri, ciki har da Goma, birni mafi girma a yankin.

Mutane da dama sun yi gudun hijira a sakamakon fadan.

Karin bayani