An kai hari a Damaturu

Gwamna Ibrahim Geidam na Jihar Yobe
Image caption Gwamna Ibrahim Geidam na Jihar Yobe

Rahotanni daga Damaturu babban birnin jihar Yobe a arewacin Najeriya na cewa, ana can ana ta jin karar musayar wuta a wata unguwa dake kan hanyar Maiduguri.

Bayanai na nuna cewa, wasu 'yan bindiga ne masu yawa suka aukawa unguwar, tun daga misalin karfe biyar na maraicen nan.

Mun yin ta buga wayar kakakin runduar JTF a jihar Yoben, Laftanar Eli Lazarus, amma ba a amsa ba.

An jima ba a kai wani hari a cikin garin Damaturu ba, amma a kwanakin baya wasu yan bindiga sun kai hari a kan makarantar koyon aikin gona ta Gujba.