Saudiya ta yi ahir ga masu neman tukin mata

Wata mace mai tuki a Saudiya
Image caption Wata mace mai tuki a Saudiya

Wani kakakin ma'aikatar cikin gida ta Saudiya ta gargadi mata cewar za a iya daukar matakai a kansu idan suka shiga cikin wani gangami a wannan mako kan hana mata tuki.

Kakakin ma'aikatar ya ce an hana mata tuki , kuma za a yi aiki da dokokin kasar ga duk wanda ya keta su ko kuma duk wani wanda yayi zanga zanga domin goyon bayan fafutikarsu.

Wani mai fafutikar neman ganin mata sun yi tukin ya shedawa BBC cewar wannan wata sanarwa ce ta dabam game da hanin tukin wadda ba ta cikin dokokin kasar ta Saudiya.

Mai fafutikar ya ce baya sa ran za a yi dauki ba -dadi da yansanda a ranar asabar a lokacin da matan suke shirin yin tukin domin nuna rashin jin dadinsu ga hanin.