'Yan Republican sun yi tayin mafita a dambarwar kasafin kudin Amurka

John Boehner
Image caption John Boehner, Kakakin majalisar wakilan Amurka

A Amurka, 'yan jam'iyyar Republican sun bada shawarar a kara yawan kudaden bashin da gwamnati za ta iya karbowa, na wucin gadi, domin gudun kada ta kasa biyan basusukan da ake binta.

Kakakin majalisar wakilai, John Boehner, ya ce zai aiwatar da matakin, in har shugaba Obama ya yarda a kara sasantawa a kan kasafin kudin kasar, wanda takaddamar da ake a kansa ta sa aka rufe wasu ma'aikatun gwamnati, a kwanaki goman da suka wuce.

A cewar kakakin fadar White House, Jay Carney, mista Obama zai duba yiwuwar sa hannu a kan yarjajeniya ta dan lokaci: Ya ce, "za mu ga irin tayin da majalisar wakilai inda 'yan Republican ke da rinjaye ta yi tukuna, kafin mu yanke hukunci."

Nan gaba manyan jam'iyyar Republican za su gana da shugaba Obama.

Shugabar asusun bada lamunin IMF, Christine Lagarde, ta yi gargadin cewa, rashin tabbas game da kasafin kudaden Amirka, zai iya yin babbar illa ga tattalin arzikin Amirkan da kuma na sauran kasashen duniya.

Ta ce, IMF bai tsoma baki a rikicin siyasar Amirkar ba.

Karin bayani