An yi harbi a kusa da majalisar dokokin Amurka

Ginin Majalisar dokokin Amurka
Image caption Ginin Majalisar dokokin Amurka

An yi harbe harbe a kusa da ginin majalisar dokokin Amurka dake birnin Washington, inda 'yan majalisar ke yi taro.

Yansanda sunce lamarin ya soma ne a lokacin da wata mata ta kwamtsa motar da take tukawa a wani shingen tsaro kusa da fadar Shugaban Amurka ta White House sannan ta sheka zuwa majalisar dokokin a Capitol Hill.

Jami'ai sunce harbin wani lamari ne na daban da ba shi da nasaba da ta'addanci.

Yansanda sunce an kama wadda ake zargi, to amma ba a bayyana halin da take ciki ba.

A halin yanzu kuma an bude majalisar dokokin , sai dai yankin ya ci gaba da zama toshe, kuma akwai yansanda da yawa a wajen.

An yi harbin ne yayinda ake ci gaba da takaddama tsakanin yan jama'iyar Democrats da ta Republican a Washington kan kasafin kudi.

Ma'aikatar kudin Amurka da kuma shugabar hukumar bayar da lamuni ta duniya -IMF sun yi gargadin cewar tattalin arzikin Amurka da na duniya za su samu mummunar illa, muddun ba a warware sabanin ba.

Ma'aikatar kudin ta ce Amurka za ta iya afkawa cikin mummunan koma bayan tattalin arziki.

A bangare guda kuma Manajin daraktar hukumar lamunin ta IMF, Christine Lagarde ta ce yana da muhimmanci a kawo karshen ja-in -jar a kan lokaci domin amincewa da adadin sabon bashin da za a kayyade wa gwamnati karba.