Hukuncin kisa kan dan majalisar Bangladesh

Image caption Salahuddin Quader Chowdhury

An yanke wa dan majalisar dokokin na bangaren adawa a kasar Bangladesh hukuncin kisa bisa zargin aikata kisan kare dangi.

Kotu ta musamman a kan laifukan yaki ta sami Salahuddin Quader Chowdhury, na jam'iyyar Bangladesh National Party (BNP) da laifin kisa lokacin yakin kokarin samun 'yancin kan kasar a wajen Pakistan a shekarar 1971.

Jam'iyyar adawa ta BNP ta ce shari'ar na da nasaba da siyasa.

A shekara ta 2010 ne gwamnatin kasar ta kafa kotun sauraron laifukan yaki, abinda jam'iyyun adawa suka bayyana a matsayin bita da kullin siyasa.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama sun ce kotun ta sabawa ka'idojin da aka sani na kasa da kasa.

Karin bayani