ICC ta bada sammacin kama Charles Ble

Image caption Charles Ble Goude

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya-ICC dake birnin Hague, ta bada sammacin kama Charles Ble Goude, wani na kusa da tsohon shugaban Ivory Coast, Laurent Gbagbo.

Ana zarginsa ne da aikata cin zarafin bil adama a shekara ta 2010 bayan zaben da ya mika ikon kasar ga mutumin da aka zaba Alassane Outtara.

Ana zargin Ble Goude ne da kasancewa mai bada horo ga mayakan sa kai da kuma wasu gungun matasa da suka muzgunawa da kuma kashe magoya bayan Alassane Outtara.

An kuma zargi gungun matasan da aikata fyade da kuma kisa.

Karin bayani