An tsare daliban Najeriya 16 a Rasha

Image caption Shugaba Goodluck Jonathan

'Yan sanda a Moscow sun tsare dalibai 'yan Najeriya 16 bisa zargin lalata wasu tebura a cikin ofishin jakadancin Najeriya, saboda kin biyansu kudaden alawus dinsu.

Ma'aikatar harkokin cikin gidan Rasha ta ce an fitar da mutanen 16 ne a cikin ofishin jakadancin bisa umurnin wasu ma'aikatan Najeriya.

Dukaninsu daliban jami'a ne a Rashar.

Wasu dalibai 'yan Afrika a baya sun yi zanga-zanga bisa kin biyansu kudin alawus daga kasashensu.

Daliban 16 da aka tsare, za su fuskanci tuhuma, kamar yadda ma'aikatar harkokin cikin gidan ta bayyana.

A bara, dalibai 'yan Najeriya sun lakadawa wakilin ofishin jakadancin duka saboda kin biyansu hakkokinsu, in ji wata jaridar Rasha lenta.ru.

Karin bayani