Ayyukan gwamnati sun tsaya cik a Amurka

Image caption An rufe hanyoyin zuwa ma'aikatun gwamnati

Ma'aikatan gwamnatin Tarayya kusan miliyan daya a Amurka suka wayi gari babu aikin yi, bayan da 'yan majalisar dokokin na jam'iyyar Republican dana Democrat suka kasa cimma matsaya a kan sabon kasafin kudi.

Fadar White House ta umurci cibiyoyin gwamnati su kasance a rufe, amma banda ayyukan da ake bukatar na gaggawa.

An bayyanawa ma'aikata su zauna a gida babu albashi, har sai 'yan majalisa sun cimma yarjejeniya.

Wannan ne karon farko cikin shekaru 17 da al'amuran gwamnatin Amurka suka tsaya cik .

Gwamnati na takun saka ne da 'yan jam'iyyar Republican wadanda ke son a yi garan bawul ga tsarin samar da lafiya na Shugaba Obama, abinda ya sa aka kasa amincewa da sabon kasafin kudin.

Karin bayani