Sana'ar daukar ciki a Indiya

Matan dake dauke da cikin wasu maza a gidan da ake kula da su
Image caption Wasu na ganin cewa talauci ne ke sa mata yanke shawarar daukar cikin wani, domin a biya su

Kudin da ake biyan matan da ake yiwa baye, domin su dauki cikin wasu mazan da ba mazajen aurensu ba ya haura dala biliyan daya a Indiya.

Kuma a lokacin da suke da juna biyun, sukan zauna ne a wani gida da masu suka ke bayyanawa a matsayin masana'antar haihuwar jarirai.

Matan na haifa wa ma'aurantan dake neman haihuwa 'ya'ya, su kuma a biya su kudi.

Tambayar a nan ita ce ko yaya mace ke ji, a lokacin da take dauke da cikin wani, domin a biya ta?

Waka a bakin mai ita

Vasanti wata matar aure ce mai shekaru 28 a duniya, kuma tana daga cikin irin wadannan matan, a cewarta "A Indiya iyali na da kusanci ta yadda a shirye ka ke ka yi duk abin da ya kama domin 'ya'yanka."

Image caption Mijin Vasanti na karabar dala 40 a wata, saboda haka kudin da zata samu zai sauya rayuwarsu

Ta kara da cewa: "Abin da ya sa na dauki cikin wani, shi ne domin in samu cika buri na game da yara na."

Vasanti na dauke da ciki ga wasu ma'aurata 'yan kasar Japan, kuma za su biya ta dala 8,000, kudin da zai isa ta gina sabon gida ta kuma tura 'ya'yanta masu shekaru bakwai da kuma biyar zuwa makarantar da ake koyar da harshen Ingilishi a kasar.

Abin da ba ta taba tsammanin za ta iya yi ba, kuma a cewarta "Ina matukar farin ciki."

An yi mata bayen ne a birnin Anand na Gujarat, kuma za ta kwashe watanni tara a wani gida da za a dinga kula da ita tare da wasu mata kamarta su goma.

Mai harkar

Wata likita, Dokta Nayna Patel ce mai asibitin da ake bayen da kuma gidan da ake kula da matan.

Image caption Matan ba su da wani iko ko tasiri a rayuwar jariran da za su haifa

"Ina fuskantar suka game da wannan abin da na ke yi mai cike da cece-kuce, akwai zargin da ake mini na cewa wai ina neman kudi ne ta wannan hanyar, wasu ma na cewa masana'antar sayar da yara, kuma sukar na da ciwo," inji Likitar.

A ganinta matan na karbar abin da ya dace, kuma ana koyar da su sana'oin hannu, saboda su samu abin dogaro bayan sun bar gidan.

Dokta Patel na yarda mace ta dauki ciki har sau uku, kuma yayin goyon cikin ba za su kusanci mazajen aurensu ba, sai dai iyalinsu za su ziyarce su sau daya a mako a yayin da suke zaman goyon ciki.

Ma'auratan da ake haifa wa jarirai kan karbe 'ya'yan da zarar an haife su, yayin da wasu lokutan su kan dauki kwanaki kafin a shirya takardun amincewa a fitar da su daga kasar.

Indiya ce kasar da ta fi kowace kasa a duniya matan dake daukar cikin wasu mazaje ta hanyar baye.