Italy: Letta ya tsallake ƙuri'ar yanke ƙauna

Praministan Italiya, Enrico Letta, ya sha daga ƙuri'ar yanke ƙauna ga gwamnatinsa a majalisar dokokin kasar a birnin Roma bayan da tsohon Praministan kasar, Silvio Berlusconi, ya sauya tunani.

Mista Berlusconi ya ce, bayan mun yi ta tattaunawa a tsakaninmu, a yanzu mun yanke shawarar amincewa da wannan gwamnati.

A da mista Berlusconin ya rantse sai ya ga bayan gwamnatin, ta hanyar janye goyon bayan jam'iyyarsa.

To amma tilas ya sunkuyo, saboda na kurkusa da shi sun yi barazanar zasu bijire masa.