Obama ya soke ziyara kasashen waje

Image caption Obama ya ce har yanzu yana duba yiwuwar kai ziyara Indonesia

Fadar gwamnatin Amurka ta ce Shugaba Obama ya soke ziyarar da zai kai kasashen Malaysia da Philippines a makon gobe domin ya fuskanci matsalar dakatar da ayyukan gwamnatin kasar.

An umarci dubban ma'aikatan gwamnatin kasar kada su je aiki bayan an rufe akasarin ma'aikatun gwamnati.

Kakakin shugaban kasar ya ce har yanzu Mista Obama yana duba yiwuwar kai ziyara kasashen nahiyar Asia - Indonesia da Brunei.

Wannan dai shi ne karo na farko da ayyukan gwamnatin tarayyar Amurka suka tsaya cik a cikin shekaru 17 da suka gabata saboda rashin samun daidaito tsakanin 'yan majalisar dokokin kasar a kan kasafin kudi.

Karin bayani