Madugun mayaka zai yi takara a Afghanistan

Mayakan Taliban na Afghanistan
Image caption Mayakan Taliban na Afghanistan

Wani madugun mayaka da ake ta cece-kuce a kansa a Afghanistan, Abdul Rassul Sayyaf ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar a zaben da za a yi a badi.

Abdul Rassul ya yaki Rasha a shekarun 1980, kuma ance yana da alaka ta kud-da kud da shugabannin kungiyar Al-qaeda ciki har da wanda ya kitsa harin da aka kai a Amurka a shekara ta 2001 da akewa lakabi da 9/11.

Har ila yau Abdul Rassul Sayyaf na daya daga cikin mutanen da suka kafa kungiyar masu kaifin kishin Islama ta Afghanistan a shekarun 1970.

Kungiyoyin kare hakkin bil'adama na zarginsa da aikata laifukan yaki.