Birtaniya ta maida martani kan Gambia

Birnin Banjul
Image caption Dama can dangantaka ta yi tsami a tsakanin Birtaniya da gwamnatin Jammeh, tun juyin mulkin da ya yi a shekarar 1994

Ma'aikatar wajen Birtaniya ta nuna rashin jin dadinta game da shawarar da kasar Gamabia ta yanke, na ficewa daga kungiyar Commonwealth shekaru 48 bayan shigarta.

Kasar ta Gambia dake yammacin Afrika ta bayyana Commonwealth dake da kasashe 54 a karkashinta, da suka hada da Birtaniya da kasashen da ta yiwa mulkin mallaka, a matsayin wani 'sabon salon mulkin mallaka.'

An sanar da ficewar kasar a gidan talabijin, amma babu wani karin bayani game da hakan.

Shekaru biyu da suka wuce ne dai shugaba Yahya Jammeh ya zargi Birtaniya da cewa, tana baiwa abokan adawarsa goyon baya gabannin babban zaben kasar.