An tsamo gawarwaki sama da 100 na 'yan cirani a Italiya

Masu aiki ceto na tsawo gawarwakin 'yan ci ranin
Image caption Mutane 300 ne ake fargabar sun mutu a hadarin jirgin ruwan

Ana fargabar cewa kimanin mutane dari uku ne suka mutu bayan wani jirgin ruwa makare da 'yan cirani da ya taso daga Afurka ya kama da wuta sannan kuma ya nutse a kan ruwan tsibirin Lampedusa na kasar Italiya.

Kawo yanzu an samu sama da gawarwaki dari, kuma masu gadin teku sun ce mutane dari da hamsin da daya ne suka tsira da ransu a hadarin.

Yayin da aka jera gawarwakin mutanen da suka mutu a wani waje a karamin tsibirin, praministan Italiyan ya bayyana sanarwar bada ranar makoki ta kasa, shi kuma paparoma wanda ya kai ziyara Lampedusan a watan Yuli, ya aike da sakon ta'aziyyarsa.

Wakilin BBC ya ce mai rike da mukamin magajin garin ta zubda hawaye ganin abin da ya faru da kuma ji daga bakin wadanda suka tsira da ransu suna bada labarin 'yar karamar wutar da aka kunna don neman taimako saboda jirgin ya samu matsala.