Hatsarin jirgin sama a Lagos

Image caption Hatsarin jirgin Dana kenan da ya hallaka mutane da dama

Rahotanni daga birnin Lagos a Najeriya na cewa, wani jirgin fasinja yayi hatsari, kuma an samu asarar rayuka.

Jirgin dai rahotanni na cewa, na kamfanin Associated Airlines ne kuma ya tashi ne daga Lagos a kan hanyarsa ta zuwa Akure, babban birnin jihar Ondo.

Yanzu haka dai 'yan kwana-kwana da kuma sauran ma'aikatan agaji suna wurin da lamarin ya auku inda ake ganin wuta tana ci.

Najeriya dai ta sha fama da hatsarin jiragen sama dake hallaka jama'a da dama.