Lampedusa: An samu tsaiko a aikin ceto

Image caption Igiyar ruwa ta kawo cikas ga masu aikin ceto

Igiyar ruwa ta tilasta wa masu aikin ceto dakatar da yunkurin da suke yi na tsamo gawarwakin 'yan ci-ranin da suka mutu a hatsarin jirgin ruwan da ya faru a kusa da tsibirin Lampedusa na kasar Italiya.

An tsamo gawarwakin fiye da mutane 100, sai dai da alama adadin mutanen da suka mutu zai ninka.

Jami'ai dai sun kawar da duk wani fata na samun mutane da ransu.

Masu aikin ceton sun bayyana cewa yanayin yana da razanarwa: gawarwaki a cunkushe waje guda, kuma wasu daga cikin gawarwakin sun makalkale a jikin allon jirgin ruwan.

Jirgin ruwan dauke da 'yan ci-rani daga kasashen Afirka ya nutse ne kusan kilomita daya kafin a kai Lampedusa.

Karin bayani