'Yan Afrika 300 sun mutu a tekun Italiya

Hatsarin jirgin ruwa tsibirin Lampedusa kasar italiya
Image caption Hatsarin jirgin ruwa tsibirin Lampedusa kasar italiya

Jami'ai masu kula da tekun kasar Italiya sun ce mutane dari uku ne suka mutu bayan wani jirgin ruwa ya nutse a gabar tekun kasar.

Jirgin ruwan makare da 'yan cirani da ya taso daga Afurka, ya kama da wuta sannan kuma ya nutse a cikin ruwan tsibirin Lampedusa na kasar Italiya.

Masu gadin teku sun ce mutane dari da hamsin da daya ne suka tsira da ransu a hadarin.

Kungiyoyin bada agaji ga 'yan gudun hijra sun kididdige cewa 'yan gudun hijirar kimani dubu 17 ne suka hallaka yayin ketare teku zuwa wasu kasashen a cikin shekaru 20.

Yawancin wadanda suka mutu a hadarin 'yan kasashen Eritrea da Somalia ne.

Hukumar 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce masu neman mafaka da suka isa Italiya a wannan shekarar sun kai dubu talatin, kuma yawanci sun taso daga kasar Libya ne.