Masu canjin kudade na kokawa a Najeriya

sanusi lamido
Image caption Babban bankin na Najeriya ya ce dole ne sai an bi ka'idojin da ya shimfida wajen shigo da kudaden waje kasar

Umarnin da Babban Bankin Najeriya ya bayar na hana shiga kasar da kudaden waje ba tare da ka'ida ba ya fara tasiri.

Wasu masu sana'ar canjin kudaden waje a kasuwannin bayan fage sun ce yanzu kasuwar ba ta gudana sosai.

Har suna fargabar cewa sana'ar tasu za ta iya durkushewa.

Sai dai Babban Bankin ya ce, dole ne a rika gudanar da komai bisa ka'ida.

kuma ya ce ya dauki wannan mataki ne don kare darajar kudin kasar da kuma tattalin arzikinta.