Rwanda ta soki Amurka kan janye tallafi

Image caption Shugaba Paul Kagame

Rwanda ta ce ta yi Allawadai da matakin da Amurka ta dauka na janye tallafin sojinta daga kasar.

Amurka ta ce za ta kakabawa Rwandar takunkumi saboda goyan gayan da take baiwa kungiyar 'yan tawaye ta M23, dake makwabciyarta Jamhuriyar demokradiyyar Congo, wadda aka yi ammanar tana amfani yara kanana su yi aikin soji.

Kakakin dakarun sojin Rwandan Joseph Nzabamwita, ya ce akwai shaidu da dama dake nuna cewa bata taba goyon bayan daukar kananan yara aikin soji.

A cewarsa, bai kamata a kama sojin Rwanda da laifin abubuwan dake faruwa a kasashen waje ba.

Karin bayani