An daure matasan da suka yi rawa zindir a Saudiyya

Image caption Sarki Abdullah na Saudiyya

Wata kotu a kasar Saudiya ta yanke wa wasu samari hudu duka hukuncin sama da bulala dubu hudu da daurin sama da shekaru 20 a kurkuku.

Kotun ta samesu da laifin nuna rashin da a wanda ya sabawa dokokin kasar ta hanyar yin rawa tsirara.

Samarin hudu sun dauki kansu a bidiyo suna rawa a kan mota, daya a cikinsu tsirara a garin Barayda dake arewa maso yammacin birnin Riyadh, suka kuma saka hotan bidiyon a shafin Youtube na yanar gizo.

Hukuncin da aka yanke wa saurayin da ya yi rawar tsirara ya fi tsauri--- inda aka bashi daurin shekaru goma a jarun, da kuma bulala dubu biyu sannan aka ci shi tarar sama da dalar Amurka dubu talatin.

Karin bayani