Sabon yunkurin Iran na diplomasiyya

jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei
Image caption jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei

Jagoran addini na kasar Iran Ayatollah Ali Khamenei ya baiyana goyon bayan yunkurin diplomasiyyar kasar na baya bayan nan.

Sai dai kuma yace wasu abubuwan da suka faru a lokacin ziyarar da sabon shugaban kasar Hassan Rouhani ya kai domin halartar taron Majalisar Dinkin Duniya a makon da ya wuce basu dace ba.

An ruwaito Ayatollah Khamenei yana cewa a shafinsa na Internet, har yanzu Iran na dari-dari da Amirkawa.

Ya baiyana gwamnatin Amirka da cewa ba abar amincewa bace.

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba