An baiyana sunayen yan bindigar Westgate

Wasu yan bindigar Westgate
Image caption Wasu yan bindigar Westgate

Hukumomin Kenya sun sanar da sunayen yan bindiga hudu wadanda suka ce sune suka kai hari a cibiyar kasuwanci na Westgate a birnin Nairobi makonni biyu da suka wuce wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da sittin da biyar.

An ga mutanen ne a hoton bidiyon da aka gano daga cibiyar kasuwancin bayan harin.

Daya daga cikinsu dan Kenya ne daya kuma dan Somalia yayin da mutum na uku kuma dan kasar Sudan ne.

Ba'a iya tantance asalin mutum na hudu ba.

Wani mai magana da yawun rundunar soji yace an kashe dukkan mutanen hudu.

Ya baiyana sunayen mutanen da cewa sune Omar Nabhan da Khattab al-Keneda Abu Baara al Sudani da kuma Umayr.

Karin bayani