'Yan tawayen Mali sun sauya shawara

'yan tawayen mali
Image caption Sabuwar gwamnatin ta Mali ta kuduri aniyar kawo karshen rikicin kasar

'Yan tawayen da suka yi watsi da yarejejniyar zaman lafiya da gwamnatin Mali a watan da ya wuce sun ce zasu sake shiga yarjejeniyar.

Kungiyar 'yan tawayen Abzinawa da kuma wasu kungiyoyin biyu sun yanke wannan shawara ne kwanaki kadan bayan da gwamnatin ta saki sama da 'yan tawaye 20.

Gwamnatin Malin ta saki mayakan ne karkashin yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla a watan Yuni.

Gurguncewar yarjejeniyar ce ta kai ga bata-kashi tsakanin 'yan tawaye da sojojin gwamnati a garuruwan Timbuktu da Kidal.

Karin bayani