Ana nuna kabilanci a jami'ar jihar kaduna

Gwamnan Kaduna Ramalan Yero
Image caption 'Yan masarautar zazzau suna kokawa da kabilancin da ake nunwa a jami'ar jihar karkashin jagorancin dan kudancin jihar

Wata kungiya ta 'yan kudancin jihar kaduna na nuna damuwa a kan abinda ta ce wani yunkuri na wasu a jahar na kara haifar da baraka tsakankanin 'yan jihar.

Kungiyar mai suna Gurara Forum,wani bangare na kungiyar ci gaban kudancin kaduna SOKAPU, na kokawa ne a bisa korafe korafen da wasu yan yankin masarautar Zazzau a bisa abinda suka ce rashin adalcin da shugaban jamiar jahar dan kudanci ke yi wa 'yan arewaci ta wajen daukar dalibai da ma'aikata.

A kwanan nan ne kungiyar masarautar zazzau din mai suna ZEMDA a takaice ta rubuta wata takardar koke ga gwamnatin jihar ta kuma buga a jaridu a bisa wannan batu, batun da yan kudancin suka ce kokarin tada zaune tsaye ne kawai.

Karin bayani