Aikin tsamo gawarwaki na ci-gaba a Lampedusa

jamiai masu aikin ceto a Lampedusa
Image caption jamiai masi aikin ceto a Lampedusa

Gwanayen nutso sun tsamo karin gawarwaki fiye da talatin daga cikin jirgin da ya nutse kusa da tsibirin Lampedusa a ranar Alhamis.

Yan ci-rani fiye da dari uku ne daga Afirka ake tsammanin sun rasu a hadarin.

Ana dai ci gaba da kokarin tsamo gawarwakin mutane daga buraguzan jirgin.

Jirgin ya nutse da zurfi cikin teku wanda hakan ya sa yan mintuna kalilan ne masu nutso ke iya yi a da'irar buraguzan jirgin a ci gaba da aikin tsamo gawarwakin.

Karin bayani